Musa Idris JB
12/04/2026
ADC Za Ta Yi ‘Zanga-Zangan Yanke Kauna’ (Civil Disobedience) Kan Amupitan Kan Neman Ya Yi Murabus Daga Shugabancin INEC
Jam'iyyar ADC na neman shugaban INEC ya yi murabus bisa zargin goon bayan APC
Jam’iyyar ADC, ta buƙaci Farfesa Joash Amupitan, ya sauka daga muƙaminsa na shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasar wato INEC.
Jam’iyyar ta yi wannan kira ne bayan wasu sabbin zarge-zarge da s**a bayyana a kan shugaban na INEC.
An ruwaito cewar wasu tsofaffin rubuce-rubucen da Amupitan ya yi a kafafen sada zumunta, sun nuna yana goyon bayan jam’iyyar APC.
Sai dai fitaccen malamin jami’ar nan ɗan Najeriya da ke zaune a Amurka, Farooq Kperogi, ya ce wasu tsofaffin rubuce-rubuce da ake alaƙanta Amupitan sun yana goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa hakan na iya rage amincewar jama’a dangane da sahihancin INEC.
Batun ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin ’yan Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta, inda ra’ayoyin mutane s**a bambanta kan gaskiyar waɗannan rubuce-rubuce.
Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce lamarin yana da matuƙar muhimmanci kuma zai iya shafar amincewar jama’a da tsarin zaɓe, inda ya buƙaci Amupitan ya yi murabus nan take.
Jam’iyyar ta kuma ce za ta ci gaba da zanga-zangan Yanke Kauna wato Civil Disobedience da ɗaukar wasu matakai har sai shugaban INEC ya sauka daga muƙaminsa.
10/02/2026
TINUBU BA ABOKINA BA NE:- El-Rufai
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya ce bai taɓa samun wata alaƙar abota ta musamman da shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Yayin wata hira da ya yi da Trust TV, El-Rufa'i ya bayyana cewa goyon bayan da ya bai wa Tinubu a zaɓen 2023 ya samo asali ne daga biyayya ga jam’iyya da yarjejeniyar siyasa, ba wai don zumunci ba.
Ya ce bayan wa’adin mulkin Buhari na shekaru takwas, akwai fahimtar cewa mulki zai koma Kudu, Tinubu ya zama ɗan takarar jam’iyya ne a wannan tsari.
02/02/2026
Kidnapped Nigerians left to Die as Poverty cuts off means of means to pay Ransoms
And People still call this type of Government Democracy?
Govt that Care for Elites and their Families is what we have in Nigeria
-Says Shariah Council President Dr Bashir Aliyu
19/01/2026
Farkon Tafiyar Ga Abunda Ya Fara Bullowa Dasu Fatawar Son Rai Da Malamai Sukamar Cha Saiya Ajiye Ya Koma Wai Mangaran-Malaman-Sunna Masu Sukar Sanarwar Yan Tatsine-Almajiran Buba-Marwa.
Allah Ya Shiryar
@2026 AFCON Final
MAROCCO Vs SENEGAL
Insha Allah
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Gombe
760214