MIAB
Ina hukuncin auri saki a muslunci
01/12/2025
اللهم آمين يارب العالمين. نسبتِ رسول اللهﷺ
In kasan bazaka jurewa zagi ba karka zagi wani
DA DUMI-DUMI || 🔥
A Yau Laraba 8 Ga Watan October, Committeen Shura Tayi Watsi Da Bukatar Sufayen Kano Cewa Sun Wakilta Shura Da Tayiwa Malam Lawan Tambayoyi A Maimakonsu Saboda Wani Babban Uzuri Da Suke Dashi Bazasu Samu Damar Zuwa Ba.
Shura Tace Bukatarsu Bata Karbu Ba Domin Wannan Ba Huruminta Bane.
Shura Ta Kara Da Cewa Wajibine Sufaye Su Ajiye Ko Wanne Irin Uzuri A Gefe Domin Suzo Su Tattauna Da Malam Lawan Triumph
kamar Yanda Jaridar Bluebarge Ta Rawaito A Yammacin Wannan Rana Ta Laraba Daga Bakin Shugaban Hukumar Shura Shehu Wada Sagagi Cewa Sunyi Allah Wadai Da Furucin Daya Futo Daga Bakin Shugaban Zawiyar "Ahbabu Rasullullahi" Sharu Abdullahi Assufiy Dake Cikin Garin Kano A Unguwar Kofar Waika
Shura Ta Kara Da Cewa Wajibine Duk Sufayen da S**a Shigar Da Karar Malam Lawan Su Shirya Zama Dashi A Kowanne Lokaci Da Shura Ta Amince Dashi in Kuma Ba Haka Ba Zasu Fuskanci Hukunci Me Tsanani Kamar Yanda Doka Ta Tanada Ga Duk Wanda Yayi Kokarin Wasa Da Hankalin Gwamnati (Shura)
ALLAH Yasakawa Gwamnan Kano (Abba Kabir Yusuf).
SAQON GAGGAWA ZUWA GA YAN AHALUSSUNNAH
Maganar dakatar da Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph Akwai lauje cikinnadi yakamata Yan uwa Ahalussunnah wannan saqon kowa Ya turashi A shafinsa sabi da saqon ya isa zuwa ga gwamnatin jahar Kano Abba Kabir Yusuf da kwamatin shura na jahar Kano
LOKACIN DA AKAI MUQABALA DA ABDULJABBAR
Har Akai muqabalar A kagama ba A dakatar dashi ba
Abduljabbar ko da A kagama muqabala bayan da wowarsa gida yaci gaba da karatuttukansa Har Sai da A kagurfanar da shi Agaban kotu Sa,annan Aka dakatar dashi
TO ABIN TAMBAYA ZUWA GA GWAMNATIN JAHAR KANO DA KWAMATIN SHURA NA KANO❓
Meyasa malam lawan Abubakar Triumph Aka da katar dashi daga gabatar da karatuttukansa
A halin ko ranar muqabalar ba,asanarba
Yakamata Yan uwa Ahalussunnah mutuhumci gwamnatin jahar Kano da kwamatin shura sui mana qarin bayani
Domin Yan uwa da yawa suna buqatar qarin bayani ❓
Game da dakatar da Sheikh Lawan Abubakar Triumph Hafizahullah
SHIN WANNAN YA KAI YA ZAMA HUJJA AKAN MAFARKIN KAAATON RAKUMI KUWA?
GA bayanin wani dan DARIKA
Ganin Manzon Allah ﷺ a Mafarki cikin Siffa dabam
Mafi kyawun fassara da na karu da ita daga Sheikh Al-Qarmawī game da ganin Manzon Allah ﷺ a mafarki cikin siffar da ba ta asali ba ita ce inda ya ce:
“Ai Tajallī ne saboda girmama Shugaban Halitta ﷺ.”
Wato, idan wani ya ga Manzon Allah ﷺ a mafarki amma ba da cikakkiyar surarsa ta hakika ba, wannan ba kuskure ba ne, sai dai wata siffa ce daga haske ko alheri nasa da Allah ya bayyana wa zuciyar mai mafarki domin daraja da kusanci.
Babban shehun Musulunci Ibn Taymiyya ya kira irin wannan mafarki da Tamsīl, inda ya ce:
"ورؤيته على شيء آخر إنما هذا تمثيل يضرب للرائي بحسب حاله"
Ma’ana: idan mutum ya ga Annabi ﷺ a mafarki amma da wani yanayi dabam, to wannan wakilci ne da aka yi wa mai mafarki gwargwadon halinsa da matsayin ruhiyarsa.
Shi kuma Imam Nawawī ya kira wannan da Ramz, ya ce:
"لأن تلك الصورة تكون رمزاً"
Ma’anarsa ita ce: wannan sura da aka gani tana zama wata alama ce ko nuni zuwa wani abu na ruhaniya. Misali, idan aka ga wata a mafarki, sannan aka ce wannan shi ne Manzon Allah ﷺ, to wannan gaskiya ne amma yana nuni da ayyukan Annabi ﷺ irin su shiryar da mutane daga duhu zuwa haske.
Sheikh Al-Qarmawī, kasancewarsa sufi, ya fi burgewa da fassarar Tajallī. Wannan yana nuna cewa wata kyakkyawar sifa daga cikin siffofin Manzon Allah ﷺ ta bayyana gare ka a mafarki, domin ƙarfafa ka a kan alheri.
Dalilan Qur’ani da Hadisi
A cikin Al-Qur’ani akwai misalai na mafarki masu nuni da alama, ba zahiri ba:
A Suratun Yūsuf (12:4), Yūsuf (AS) ya ga rana, wata, da taurari suna yi masa sujada. Wannan ba ainihi ba ne, sai dai wakilci ne na iyalinsa.
A Suratun As-Saffāt (37:102-105), Ibrāhīm (AS) ya ga yana yanka ɗansa a mafarki. Wannan ba da gaske aka yi ba, sai dai umurnin Allah ne da aka nuna a mafarki, daga baya kuma aka sauya shi da rago.
A cikin hadisi kuwa, Annabi ﷺ ya ce:
“Duk wanda ya ganni a mafarki, to ya ganni ne hakika, domin Shaidan ba zai iya ɗaukar sifata ba.” (Bukhari da Muslim).
Malamai sun yi bayani cewa wannan hadisi yana nufin idan aka ganshi da siffarsa ta gaskiya (irin yadda aka bayyana shi a hadisi: fata, tsawo, gemu, da sauransu). Idan kuma aka ganshi da wani hali dabam, to wannan ishara ce da ke nuni da wani abu, ba karya ba.
Sharhin Malamai
Ibn Hajar al-‘Asqalānī ya ce: “Idan aka ganshi da sifarsa ta hakika, wannan gaskiya ce; idan kuwa aka ganshi dabam, to wannan ishara ce da nuni ga wani al’amari.”
Al-Qādī ‘Iyād ya ce: “Idan aka ganshi da siffa ba ta gaskiya ba, to hakan yana nuni da ma’ana, kamar mafarkin Yūsuf da iyalinsa.”
Sheikh Al-Qarmawī ya ce: “Ai wannan Tajallī ne haske daga siffofin Annabi ﷺ ya bayyana ga zuciyar mai mafarki, domin girmama shi.”
Ma’anar Kalmomin
Tamsīl – wakilci ko misali (Ibn Taymiyya).
Ramz – alama ko ishara (Imam Nawawī).
Tajallī – bayyana wani haske daga siffofin Annabi ﷺ (Sheikh Al-Qarmawī).
Dukkan su suna nuni zuwa abu guda: ganin Annabi ﷺ da sura dabam ba wai karya ba ne, illa alama ce daga Allah.
Darussa
1. Ganin Annabi ﷺ a mafarki alama ce ta alheri da rahama.
2. Idan aka ganshi da cikakkiyar sifarsa wannan gaskiya ce kai tsaye.
3. Idan aka ganshi da wani yanayi dabam wannan ishara ce zuwa ga wani sako .
4. Mafarki bai taɓa sabawa shari’a ba – duk mafarkin da ya saba Qur’ani ko Sunnah ba daga Allah ba ne.
A takaice: Ibn Taymiyya ya kira shi Tamsīl, Nawawī ya kira shi Ramz, Sheikh Al-Qarmawī ya kira shi Tajallī. Amma dukkan malamai sun yarda cewa idan aka ga Annabi ﷺ a mafarki cikin siffa dabam, to wannan wata alama ce daga Allah domin nuna alheri, gargadi, ko daraja.
TAMBAYA GA MASU ƘOƘARIN KARE ƘARMAWI...
Wai sun ce: Ai larabawa na yabon manyan mutane da raƙumi saboda ɗaukar nauyin jama'ar su, sai nace:
Shi kuma wannan kai tsaye yace: In kayi mafarki kaga ƙaton raƙumi toh shi ka gani...
Ba a yabo ya faɗa ba, ballantana muce tashbihi yayi, kai tsaye ya nuna cewa in kaga raƙumi shi ka gani (Wa iyazubillah!!)....
Tambaya a nan a ina aka fassara mafarkin cewa raƙumi na zama fiyayyen halitta??
In baku gane ba, a ina aka ce in kaga ƙaton raƙumi to shi ne??
A bamu amsa kan abin da Ƙarmawiy ya tabbatar, ba tare da boris ba, da Hujja daga Alƙur'ani ko Sunnah, ko fassarar mafarkin magabata.... .............
Wato in kana neman masu maida ƙarya gaskiya, da lauye wuyan gaskiya zuwa ƙarya to ka samu Sufaye...
A ƙarshe menene hukuncin wanda shi kuma ya siffanta Annabi S.A.W da hankaka??!!
Da wanda yace: In ka ga shehun ka to shi ka gani...
Da wanda yace tsawa dariyar sa ce...
Shin shima wannan duka a cikikn yabo ne??
In amsar ka ta zama Eh, to a bamu amsar da dalilai...
Wassalam
Son manzon Allah ibada ne
MIAB wayar da kan al'umma
01/10/2025
Ya Allah ka azirta mu da soyayyar manzon Allah
Click here to claim your Sponsored Listing.